Gamal Gorkeh Nkrumah, ɗan tsohon shugaban kasar Ghana na farko, Kwame Nkrumah, ya rasu yana da shekara 68 a birnin Alkahira na ƙasar Masar, bayan fama da doguwar jinya.
DW Africa ta rawaito cewa Gamal ya rasu kamar yadda wasu majiyoyi daga iyalinsa suka bayyana, bayan ya shafe wani lokaci yana jinya.
An haifi Gamal a birnin Accra na Ghana, ga Kwame Nkrumah da matarsa Fathia Nkrumah.
Marigayin ya shahara a fannin aikin jarida, inda ya shafe sama da shekaru 15 yana aiki a matsayin editan labarai da marubucin sharhi a jaridar Al-Ahram Weekly ta ƙasar Masar.
A tsawon aikinsa, Gamal ya yi rubuce-rubuce kan siyasar Afirka, al’amuran ƙasashen duniya da kuma manufar haɗin kan al’ummar Afirka, wadda aka fi sani da Pan-Africanism.
An san shi da rubuce-rubucen da suka mayar da hankali kan matsalolin da nahiyar Afirka ke fuskanta, da kuma rawar da ƙasashen Afirka za su iya takawa wajen tsara makomarsu.
Mahaifinsa, Kwame Nkrumah, na daga cikin manyan jagororin gwagwarmayar neman ’yancin kai a Afirka, kuma ya zama shugaban Ghana na farko bayan samun ’yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1957.
Gamal ya gudanar rayuwarsa ta aikin jarida a Masar, inda ya bayar da gudummawa wajen tattauna batutuwan siyasa da zamantakewar al’umma ta hanyar rubuce-rubucensa.
Iyalansa sun bayyana cewa za a yi jana’izarsa a Masar a ranar 17 ga Oktoba, 2026, bisa koyarwar addinin Musulunci.
