DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiDSS ta cafke tsohon Ministan Tinubu a filin jirgin jihar Enugu

DSS ta cafke tsohon Ministan Tinubu a filin jirgin jihar Enugu

Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) sun kama tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, a Filin Jirgin Sama na Akanu Ibiam da ke Enugu.

Rahotanni sun ce an kama Nnaji ne da safiyar Laraba yayin da yake shirin shiga wani jirgin sama mai zaman kansa zuwa Abuja.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa DSS ta gudanar da kamen ne bisa buƙatar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), wadda ke bincikensa kan wasu zarge-zarge.

Bayan kama shi, an miƙa Nnaji ga jami’an ICPC domin ci gaba da bincike.

Majiyoyin sun ce tun da farko ICPC ta gayyaci tsohon ministan sau da dama bayan samun koke-koken da ke zargin an tafka ba-daidai ba wajen tafiyar da Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha a lokacin da yake jagoranta.

Sai dai sun ce bayan ya gaza amsa gayyatar hukumar, ICPC ta nemi taimakon DSS domin kamo shi.

Uche Nnaji dai ya yi murabus daga mukamin Ministan Kimiyya da Fasaha a watan Oktoban bara, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a lokacin.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, DSS da ICPC ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan kamen ba, yayin da shi ma tsohon ministan bai yi wani martani kan zarge-zargen da ake masa ba.

Haka kuma, ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun ICPC, John Odeh, bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran waya ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata