Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin bankunan bayar da rancen kudi 46 daga ranar 1 ga Yulin 2026.
CBN ya ce an ɗauki matakin ne bisa tanadin Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kuɗi (BOFIA) ta 2020, bayan bankunan sun gaza cika ƙa’idojin da ake buƙata domin ci gaba da gudanar da aiki.
A cewar CBN, Gwamnan bankin, Olayemi Cardoso, ya amince da soke lasisin bankunan bayan bincike ya nuna sun kasa cika sharuddan aiki.
Bankin ya bayyana cewa wasu daga cikin dalilan sun haɗa da rashin isassun kadarori don biyan basussuka, dakatar da aiki ba tare da izinin CBN ba, da kuma daina gudanar da harkokin kuɗi.
Sauran dalilan sun haɗa da kasa fara aiki cikin watanni 12 bayan samun lasisi da kuma gaza riƙe mafi ƙarancin jarin da doka ta tanada.
CBN ya ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarinsa na kare masu ajiya, tabbatar da zaman lafiyar tsarin kuɗi da kuma tilasta bin dokokin da suka shafi cibiyoyin kuɗi.
Bankin ya jaddada cewa zai cigaba da sa ido tare da ɗaukar matakan da suka dace domin kare amincewar jama’a da tsarin kuɗin Nijeriya.
Daga cikin bankunan da abin ya shafa akwai Bompai Microfinance Bank, Zain Microfinance Bank (tsohon Dawakin Tofa MFB), Ajwa Microfinance Bank, Minjibir Microfinance Bank, Esteem Microfinance Bank, da sauran bankuna daga jihohi daban-daban na ƙasar.
