DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 2, 2026
HomeWasanniFA na duba matakin da ya dace ta ɗauka game da hukunci...

FA na duba matakin da ya dace ta ɗauka game da hukunci kan Man City

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila (FA) ta ce hukuncin da wata hukumar bincike mai zaman kanta ta yanke kan Manchester City na da babban tasiri kan amincin wasan ƙwallon ƙafa.

Jaridar Punch ta ruwaito FA ta ce tana nazarin hukuncin da aka yanke da kuma abubuwan da ka iya biyo bayansa, tana mai cewa za ta ɗauki matakin da ya dace idan ya zama dole.

Hakan na zuwa ne bayan hukumar binciken ta samu Manchester City da laifin karya wasu dokokin kuɗi na gasar Premier League a tsawon shekaru tara.

Premier League ta ce binciken ya gano cewa Manchester City ta kulla wasu yarjejeniyoyin bogi da abokan hulɗar kasuwanci, ta gabatar da bayanan kuɗi da ba su dace ba, tare da ɓoye ainihin halin kuɗaɗenta ga masu binciken asusu da hukumomin ƙwallon ƙafa.

Hukumar binciken ta kuma ce ƙungiyar ta karya ƙa’idojin kashe kuɗi na Premier League da UEFA a a lokuta da dama, sannan ta tabbatar da uku daga cikin zarge-zarge huɗu da suka shafi yadda City ta ba da haɗin kai ga binciken Premier League.

A yanzu dai Premier League ba ta sanar da irin hukuncin da za a ɗauka kan waɗannan laifuka ba, yayin da Manchester City ke da damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

Hakazalika, Ƙungiyar ta ƙi amincewa da zarge-zargen, tana mai cewa ba ta aikata laifin da ake tuhumarta da shi ba.

A cikin sanarwar da ta fitar ranar Juma’a, FA ta ce ba za ta yi ƙarin bayani ba yayin da shari’ar tsakanin Premier League da Manchester City ke ci gaba, amma ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sa ido kan lamarin tare da ɗaukar mataki “inda ya dace”.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata