DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeKasuwanciFarashin gangar ɗanyen mai ya fadi zuwa dala 92 a duniya

Farashin gangar ɗanyen mai ya fadi zuwa dala 92 a duniya

Farashin gangar danyen man fetur ya fadi zuwa kusan dala 92 a kasuwannin duniya, bayan dakatar da hare-haren da aka shafe kwanaki ana gwabzawa tsakanin Amurka da Iran, lamarin da ya kara haifar da fatan komawa tattaunawar sulhu da kuma sake bude mashigar ruwan Hormuz.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa farashin danyen man ya ragu da kashi 5.2 cikin 100 zuwa kusan dala 92 kan kowace ganga, yayin da danyen man West Texas Intermediate na Amurka ya sauka da kashi 5.4 cikin 100 zuwa dala 84.45 kan kowace ganga.

Rahoton ya ce bayan kwanaki 13 ana kai hare-hare kan wasu wurare a Iran, Amurka ta dakatar da hare-haren a karshen mako, yayin da wakilin Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa Shugaba Donald Trump ya ba tattaunawar diflomasiyya damar ci gaba.

A nata bangaren, gwamnatin Iran ta sanar da dakatar da hare-haren ramuwar gayya kan kasashen makwabta, matakin da ya rage fargabar da ake da ita kan zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma samar da danyen mai a yankin Gulf.

Rikicin ya sake barkewa ne bayan Iran ta kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke bi ta mashigar Hormuz, abin da ya janyo karin tashin hankali a yankin.

Daga bisani kuma mayakan Houthi masu samun goyon bayan Iran sun kai hare-hare kan jiragen ruwan Saudiyya a mashigar Bab al-Mandeb.

Wannan rikici ya sa farashin danyen mai ya haura dala 100 kan kowace ganga a makon da ya gabata, kafin ya fara sauka bayan rahotannin da suka nuna cewa zirga-zirgar jiragen ruwa ta ci gaba ba tare da tangarda ba.

Rahoton ya kuma bayyana cewa Iran ta ce ta samu ci gaba a tattaunawar da take yi da kasar Oman kan yadda za a tabbatar da tsaro da ci gaba da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz tare da mutunta ikon kasashen biyu.

Haka kuma, wasu rahotanni sun nuna cewa kasar Pakistan na kokarin sake farfado da tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran, bayan wani yunƙuri da kasar China ta fara.

Masana tattalin arziki sun bayyana cewa raguwar tashin hankali a Gabas ta Tsakiya ya rage fargabar karin hauhawar farashi a duniya da yiwuwar kara yawan kudin ruwa da manyan bankunan duniya za su yi.

Sai dai har yanzu masu zuba jari na ci gaba da sanya ido kan rahotannin ribar manyan kamfanonin fasaha da kuma matakan da babban bankin Amurka zai dauka kan manufofin kudi a wannan mako.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata