Kwamitin kasafi kudi na Majalisar Wakilai ta Amurka ya amince da wasu sabbin tanade-tanade a kudirin kasafin ma’aikatar harkokin waje da suka ƙara tsaurara sa ido da sharuddan tallafin kuɗi ga Nijeriya.
Wannan na kunshe ne cikin kudirin kasafin shekarar 2027 da ya shafi tsaro da harkokin ƙasashen waje, wanda kwamitin ya amince da shi a ranar Laraba. ‘Yan majalisar sun danganta matakin da zargin cewa gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba ta yi isasshen kokari wajen dakile hare-haren da ke shafar al’ummomin Kirista ba, ciki har da hare-haren da ake dangantawa da wasu kungiyoyin Fulani da kuma ‘yan ta’adda.
A cikin kudirin, an ware dala biliyan $6.89 domin shirye-shiryen tsaron kasa, inda akalla kashi 15 cikin 100 za a bai wa Afirka; sai dala miliyan $870 don yaki da ta’addanci da hana yaduwar makamai; dala miliyan $119.15 domin horas da sojoji; da kuma dala biliyan $1.66 domin yaki da miyagun kwayoyi da tabbatar da doka.
Sai dai kudirin bai fayyace takamaiman adadin da za a bai wa Nijeriya ba. Maimakon haka, ya tanadi cewa kashi 50 cikin 100 na duk wani tallafi da aka ware wa Nijeriya za a dakatar da shi har sai an tabbatar cewa gwamnati na daukar matakan da suka dace wajen dakile rikicin addini.
Haka kuma, kudirin ya bukaci a yi amfani da kudaden wajen bincike da gurfanar da wadanda ake zargi da aikata hare-haren, ciki har da kungiyoyin da ake dangantawa da Fulani. Har ila yau, ya jaddada cewa dole ne gwamnati ta samar da hanyoyin dawowar mutanen da rikice-rikice suka raba da gidajensu cikin aminci.
Bugu da kari, kudirin ya tanadi cewa gwamnatin Nijeriya za ta rika ba da nata gudunmawar kuɗi daidai da adadin da Amurka ke kashewa kan shirye-shiryen da ake gudanarwa a ƙasar.
