Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga al’ummar jihar da su guji duk wani abu da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali yayin da babban zaben 2027 ke kara karatowa.
Jaridar Punch ta ruwaito Gwamnan ya yi wannan kiran ne a cikin jawabin da ya gabatar a wajen bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Nijeriya, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha a ranar Alhamis.
Abba Yusuf ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da rungumar zaman lafiya, hadin kai da mutunta juna, yana mai cewa wadannan abubuwa na da muhimmanci wajen bunkasar tattalin arziki da ci gaban Kano.
Ya kuma bukaci ’yan Nijeriya da su ci gaba da yin addu’ar ganin an gudanar da zaben 2027 cikin lumana, cikin ’yanci, adalci da gaskiya.
Gwamnan ya ce ya kamata al’umma su yi watsi da tashin hankali, rarrabuwar kai, rashin hakuri da aikata laifuka.
Kazalika ya yaba wa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da sojoji, ’yan sanda, NSCDC da DSS, musamman a yankunan da ke fuskantar matsalolin tsaro.
Ya ce gwamnatin jihar ta kara karfafa tsarin hadin gwiwar tsaro a kananan hukumomi da dama, ciki har da Tsanyawa, Ghari, Gwarzo, Shanono, Bagwai, Rogo, Kiru/Bebeji, Karaye da Tudun Wada/Doguwa, domin kare rayuka da taimaka wa manoma su koma harkokinsu.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki matakai kan matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar su, tare da kafa rundunar hadin gwiwa ta musamman kan miyagun kwayoyi.
Ya ce gwamnati ta kuma tallafa wa dubban iyalai ta hanyar basu jari, dabbobi, sana’o’i da sauran tallafi domin inganta rayuwarsu.
