DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijeriya na ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro – Ministan tsaro

Gwamnatin Nijeriya na ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro – Ministan tsaro

Ministan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatar wa ’yan ƙasar mazauna ƙasashen waje cewa gwamnatin tarayya na ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa tsaron ƙasa domin tabbatar da zaman lafiya da samar da yanayin da zai ba ’yan ƙasar damar ziyartar gida cikin kwanciyar hankali.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ’yan Nijeriya da ke zaune a Angola, inda ya ce gwamnati na ƙara yawan jami’an tsaro tare da inganta kayan aiki da ƙarfin rundunar sojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro.

Ganawar ta gudana ne a Luanda, Angola, yayin da ake gudanar da zama na musamman na 21 na taron shugabannin kasashe da Gwamnatocin tarayyar Afirka (AU).

Tawagar Nijeriya a taron AU ta samu jagorancin mataimakin Shugaban kasar, Kashim Shettima, inda wakilan gwamnati suka saurari koke-koken ’yan Nijeriya mazauna Angola tare da ba su amsoshi kan wasu daga cikin matsalolin da suka gabatar.

Ministan tsaron ya yaba wa al’ummar Nijeriya da ke Angola kan yadda suke gudanar da kyakkyawar alaƙa da ofishin jakadancin Nijeriya a ƙasar.

Ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da cikakken ƙudurin magance barazanar tsaro da ke fuskantar ƙasar, yana mai cewa gwamnati na ɗaukar matakai a sassa daban-daban domin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa.

A cewarsa, wasu daga cikin matsalolin tsaro da Nijeriya ke fuskanta suna da alaƙa da rashin zaman lafiya a yankin Sahel, wanda ke iya tsallakawa zuwa ƙasashen da ke makwabtaka da yankin.

Janar Musa ya ce gwamnati na aiwatar da tsauraran matakan kula da iyakokin ƙasa domin dakile kutsen masu aikata laifuka da sauran barazanar tsaro daga ƙasashen waje.

Ya kuma jaddada muhimmancin amfani da sahihan bayanai wajen tsara dabarun tsaro da shirye-shiryen ci gaban ƙasa, yana mai cewa ƙoƙarin gwamnati na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya yana ci gaba.

A nasa ɓangaren, ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa gwamnati ta inganta tsarin kare bayanan jama’a da kuma hanyoyin tantance ɗan ƙasa.

Shugabar ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta kuma tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa ƙofofin hukumar a buɗe suke domin tallafa musu da kuma samar da damammaki da za su amfani ƙasa da ’yan ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata