DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, October 8, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tinibu ta roƙi ƴan kasuwar ƙarafa su dakatar da yajin aiki

Gwamnatin Tinibu ta roƙi ƴan kasuwar ƙarafa su dakatar da yajin aiki

Gwamnatin Nijeriya ta roƙi ƴan kasuwar ƙarafa ƙarƙashin ƙungiyar dillalan kasuwar ƙarafa (NASWDEN) da su dakatar da yajin aikin da suke yi, tare da komawa teburin tattaunawa domin warware matsalolin da ke barazana ga harkokin masana’antar ƙarafa a ƙasar.

Ministan Bunƙasa Masana’antar Ƙarafa, Yarima Shuaibu Audu, ya yi wannan roƙo ne ta hannun Babban Sakataren ma’aikatar, Ambasada Nura Abba Rimi, a cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ma’aikatar, Tine-Iulun M.A., ya fitar ranar Alhamis, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne bayan da mambobin NASWDEN suka shiga yajin aiki kan abin da ƙungiyar ta bayyana a matsayin wasu matakai da ke kawo cikas ga ayyukansu da kuma muradun tattalin arziƙinsu a harkar saye da sayar da ƙarafa.

Daga cikin ƙorafe-ƙorafen ƙungiyar akwai zargin rage darajar ƙarafa,
magudi a na’urorin auna nauyi wanda ke janyo rage nauyin ƙarafan da aka saya, da kuma sayen ƙarafa kai tsaye daga dillalai da kamfanonin ƙarafa na cikin gida da sauran masu sarrafa ƙarafa. Haka kuma, ƙungiyar ta koka kan shigo da billets daga ƙasashen waje.

Gwamnatin Tarayya ta ce ta fahimci damuwar da dillalan ƙarafan suka bayyana, kuma tana duba ƙorafe-ƙorafen tare da tuntubar Majalisar Ƙarafa ta Ƙasa.

Ministan ya ce yaji ƙorafe-ƙorafen da NASWDEN ta gabatar wa ma’aikatar ta hannun Majalisar Ƙarafa ta Ƙasa.

Ƙorafe-ƙorafen sun haɗa da zargin rage darajar ƙarafa, rage nauyin ƙarafan sakamakon magudi da ake zargin ana yi da na’urorin awo, shiga kai tsaye da kamfanonin ƙarafa na cikin gida da sauran kamfanonin da ke samar da ƙarafa wajen sayen tarkacen ƙarafa, shigo da billets, da sauran matakan da ƙungiyar ke ganin suna hana dillalan ƙarafa damar taka muhimmiyar rawa a tsarin samar da ƙarafa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata