DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, October 8, 2026
HomeBabban Labari Tabbas sauye-sauyen Tinubu sun jefa ƙarin ƴan Nijeriya cikin talauci - Bwala

Tabbas sauye-sauyen Tinubu sun jefa ƙarin ƴan Nijeriya cikin talauci – Bwala

Babban mai ba shugaban ƙasa Bola Tinubu Shawara kan sadarwa Daniel Bwala, ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziƙin da gwamnati ta aiwatar sun jefa ƙarin ƴan Nijeriya cikin talauci.

Sai dai ya dage cewa ƙasar ta samu “babban ci gaba” tun bayan fara aiwatar da sauye-sauyen.

Bwala ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan tasirin cire tallafin man fetur da kuma sauye-sauyen da aka yi a tsarin canjin kuɗin waje.

Ya ce, ya kamata hatta ƴan adawa su fahimci cewa dalilin da ya sa ake da wannan adadi na talakawa da kuma wasu hasashe na bala’i da mutane ke yi, shi ne saboda mun aiwatar da sauye-sauye.

Bwala ya ce ba za a iya kallon ƙarin talauci ba tare da la’akari da sake fasalin tattalin arziƙin da gwamnatin ta aiwatar ba.

Ya ƙara da cewa, “Saboda haka, ba za ku iya yin watsi da cewa akwai mutane da dama a cikin al’ummarmu da ke cikin talauci ba, domin mun amince da hakan, amma mun samu ci gaba zuwa yanzu.”

Wannan furuci na Bwala na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da samun saɓani tsakanin masana tattalin arziƙi, ’yan siyasar adawa da gwamnatin tarayya kan sakamakon sauye-sauyen.

Bankin Duniya ya amince cewa Nijeriya ta samu ci gaba a fannin tattalin arziƙin ƙasa baki ɗaya bayan sauye-sauyen, ciki har da inganta ma’aunin kuɗaɗen waje, kyautata yanayin kuɗaɗen gwamnati da kuma ci gaba da bunƙasar tattalin arziƙi.

Sai dai bankin ya yi gargaɗin cewa har yanzu waɗannan nasarorin ba su isa su haifar da gagarumin sauƙi a rayuwar miliyoyin ƴan Nijeriya ba.

Bankin ya kiyasta a shekarar 2025 cewa yawan ƴan Nijeriya da ke fama da talauci ya ƙaru sosai a shekarun da suka gabata, sai dai ya bayyana cewa yawancin ƙarin talaucin ya faru ne kafin gwamnatin Tinubu ta hau mulki

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata