DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabarai'Yan sanda sun yi nasarar ajalin 'yan bindiga a Abuja

‘Yan sanda sun yi nasarar ajalin ‘yan bindiga a Abuja

Jami’an rundunar ’yan sandan birnin tarayya Abuja sun samu nasarar hallaka wasu ’yan bindiga biyu tare da kubutar da mutane biyar da aka yi garkuwa da su a yankin Bwari.

Kwamishinan ’yan sandan Abuja , CP Ahmed Mohammed Sanusi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba, inda ya ce shi da kansa ne ya jagoranci aikin da ya kai ga nasarar farmakin.

A cewarsa, jami’an tsaron sun fara bin diddigin gungun ’yan bindigar ne bayan harin da suka kai wa al’ummar kauyen Paze da ke mazabar Byazhin a karamar hukumar Bwari a makon da ya gabata.

An rawaito cewa a lokacin harin, ’yan bindigar sun yi awon gaba da mutane biyar ciki har da wani fasto, yayin da suka harbe wani jami’in sintirin sa-kai mai suna Shuaibu Yerima har lahira.

Kwamishinan ya ce an gudanar da aikin ne tare da hadin gwiwar jami’an sashen yaki da garkuwa da mutane, rundunar IRT na yankin Kubwa, da kuma mafarauta da masu aikin sa-kai na yankin.

Ya bayyana cewa da misalin karfe 9:00 na dare a ranar Talata ne tawagar hadin gwiwar ta kaddamar da wani samame a yankunan Paze da Byazhin domin ceto wadanda aka sace da kuma cafke maharan.

A yayin aikin, jami’an tsaron sun yi artabu da ’yan bindigar, inda aka halaka biyu daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere zuwa tsaunuka da dazukan da ke kusa da yankin.

Kazalika, jami’an sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a garkuwar, wadanda aka bayyana sunayensu da Icheh Mohammadu da Abubakar Usman, tare da kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu da harsasai.

CP Sanusi ya ce an garzaya da mutanen da aka ceto zuwa asibiti domin duba lafiyarsu, yayin da ake shirye-shiryen mayar da su ga iyalansu bayan kammala kula da lafiyarsu.

Ya kara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da sintiri da bincike a yankunan domin cafke sauran wadanda suka tsere, tare da rusa gaba daya wuraren ayyukan ta’addancin kungiyar.

Haka kuma ya bukaci asibitoci da ma’aikatan lafiya su rika sanar da jami’an tsaro duk wanda ya zo neman magani sakamakon raunin harbin bindiga ko kuma cikin yanayi mai tayar da hankali.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata