Likitoci a Jihar Lagos sun gudanar da wata zanga-zanga ta musamman domin nuna rashin jin daɗinsu kan abin da suka kira ci gaba da muzgunawa, tsoratarwa da kuma kama su ba bisa ka’ida ba daga jami’an tsaro, musamman ‘yan sanda.
Kamar yadda rahotanni suka nuna, zanga-zangar ta samu jagorancin Ƙungiyar Likitocin Nijeriya (NMA) reshen Lagos da kuma Ƙungiyar Likitocin Masu Asibitoci Masu Zaman Kansu (ANPMP), inda likitocin suka yi tattaki daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Lagos (LASUTH) zuwa hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar da ke Ikeja.
Jaridar The Sun ta ruwaito cewa shugaban ANPMP a Lagos, Dokta Jonathan Esegine, ya bayyana zanga-zangar a matsayin mai muhimmanci, yana mai cewa an tilasta musu fitowa ne saboda yadda ake kama likitoci daga wuraren aikinsu tare da tsare su ba tare da dalili ba.
Ya ce irin wannan hali na iya jefa lafiyar al’umma cikin haɗari, domin wasu lokuta ana kwashe likitoci daga wajen kula da marasa lafiya, wanda hakan ke sa a dakatar da ayyukan jinya.
Esegine ya kuma ce wannan yanayi na sa likitoci tsoron ɗaukar wasu matakan gaggawa yayin kula da marasa lafiya, saboda fargabar cewa idan wani abu ya faru za a iya kama su ko zarginsu da laifi.
Shi ma shugaban NMA a Lagos, Dokta Babajide Saheed, ya yi Allah-wadai da abin da ya kira muzgunawar hukumomi da kuma shari’ar kafafen sada zumunta, yana mai kira ga manema labarai su rika tabbatar da gaskiyar labarai kafin wallafawa.
Rahotanni sun ce zanga-zangar ta biyo bayan tsare wani likita da wata jinya a Lekki bayan mutuwar wasu yara biyu masu fama da matsananciyar gudawa duk da kokarin da aka yi na ceton su.
