DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 19, 2026
HomeLabarai‘Yan bindiga sun sace basarake da matarsa a Kwara

‘Yan bindiga sun sace basarake da matarsa a Kwara

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari fadar wani sarki a ƙauyen Olayinka da ke Ƙaramar Hukumar Ifelodun a Jihar Kwara, inda suka sace sarkin tare da matarsa da wani mutum guda a wani harin tsakar dare.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, maharan da ake cewa suna dauke da makamai sun kutsa cikin fadar Oba Salman Aweda da misalin ƙarfe 1:40 na dare ranar Asabar, inda suka rika harbe-harbe domin tsoratar da mazauna yankin kafin su tafi da sarkin da wasu mutane biyu zuwa wurin da ba a sani ba.

Mazauna yankin sun ce harin ya jefa al’umma cikin firgici, domin maharan sun zo da yawa kuma babu wanda ya iya tunkarar su lokacin da suka kai harin.

Sarkin Ora, Oba Rilwan Yekini, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa harin na nuna yadda matsalar tsaro ke kara tsananta a yankunan da ke kusa da juna a jihar.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Ifelodun, Hadji Abdulrasheed Yusuf, ya ce gwamnati na aiki tare da jami’an tsaro domin ceto waɗanda aka sace, inda aka fara wani samame na hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro, masu gadin dazuzzuka da kuma ‘yan sa-kai domin neman maharan.

Haka kuma, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Adekimi Ojo, ya ce jami’an tsaro sun kara matsa lamba kan masu garkuwar da mutane, yana mai cewa ana zargin wasu masu taimaka wa ‘yan bindigar daga cikin al’umma amma jami’an tsaro na bibiyarsu.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata