Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya ICPC, ta ce tana bibiyar ayyukan mazabu 21 da darajarsu ta haura Naira biliyan daya a fadin jihar Katsina.
Ayyukan, wadanda jimillar kudinsu ta kai N1,025,573,139.96, na cikin wadanda hukumar ke sanya ido a kansu domin tabbatar da gaskiya, rikon amana da kuma ganin an samu amfanin kudaden gwamnati da aka kashe wajen aiwatar da ayyukan mazabu.
Shugaban tawagar ICPC mai bibiyar ayyukan, Dr. Murtala Bankanu, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Katsina. Ya ce aikin bibiyar ya shafi shiyyoyin Katsina da Funtua da kuma mazabun tarayya 10 a fadin jihar.
Mazabun sun hada da Daura/Sandamu/Mai’adua, Baure/Zango, Mashi/Dutsinma, Batagarawa/Charanchi/Rimi, Malumfashi/Kafur, Dutsinma/Kurfi, Katsina Central, Funtua/Dandume, Faskari/Sabuwa/Kankara da Musawa/Matazu.
Dr. Murtala ya ce ayyukan da ake bibiyar sun shafi muhimman bangarori da suka hada da ilimi, noma, lantarki, samar da ruwa, kiwon lafiya da shirye-shiryen karfafa tattalin arzikin al’umma.
A bangaren ilimi, ayyukan sun hada da rabon littattafai, kayan makaranta da sauran kayayyakin karatu da aka tanada domin tallafa wa dalibai tare da inganta yanayin koyarwa da koyo.
A bangaren samar da ruwa kuwa, hukumar ta duba ayyukan rijiyoyin burtsatse da aka tanada domin samar wa al’umma ruwan sha mai tsafta da rage matsalolin karancin ruwa.
Ayyukan noma sun hada da rabon buhunan taki da sauran tallafin da aka tanada domin taimaka wa manoma da bunkasa harkokin noma a yankunan da suka ci gajiyar shirin.
Haka kuma, ayyukan bangaren lantarki sun hada da samarwa da girka na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana, yayin da bibiyar ta kuma shafi ayyukan kiwon lafiya da shirye-shiryen tallafa wa al’umma domin dogaro da kai.
Dr. Murtala Bankanu ya ce manufar aikin bibiyar ita ce tabbatar da ko an yi amfani da kudaden da aka ware domin ayyukan yadda aka tsara, da kuma ko al’ummomin da aka tanada domin su amfana sun samu ayyukan.
Ya kara da cewa, hukumar za ta tabbatar da ko ayyukan da aka bayyana cewa an kammala su an aiwatar da su a wuraren da aka tsara. Idan kuma an aiwatar da aikin, jami’an za su tantance ko an yi shi bisa ka’idoji, girma da ingancin da aka amince da su.
Ya ce ‘yan kwangilar da aka gano sun yi watsi da ayyuka, suka yi aiki mara inganci ko kuma suka saba wa ka’idojin da aka amince da su, za a bukaci su koma wuraren ayyukan domin gyara matsalolin da aka gano.
