DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiDSS ta yi gargadi kan barazanar kai hari manyan makarantu a Sokoto

DSS ta yi gargadi kan barazanar kai hari manyan makarantu a Sokoto

Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya, DSS, reshen jihar Sokoto, ta yi gargadin cewa tana da bayanan sirri da ke nuna yiwuwar wasu kungiyoyin ’yan ta’adda da ’yan bindiga na shirin kai hare-hare da yin garkuwa da mutane a manyan makarantun jihar.

Gargadin na cikin wata wasika da hukumar ta aike wa gwamnatin jihar Sokoto a ranar 18 ga Yuli, 2026, inda ta ce ’yan ta’adda da ’yan bindiga sun sauya salon kai hare-harensu daga makarantun firamare da sakandare zuwa jami’o’i da sauran manyan makarantu.

A cewar DSS, wannan sabuwar barazanar na iya jefa dalibai, malamai, sauran ma’aikata da kuma iyalansu cikin hadarin garkuwa da su ko fuskantar wasu hare-hare, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Hukumar ta ce hakan na daga cikin yunkurin kungiyoyin masu aikata laifuka na kawo cikas ga harkokin ilimi, raunana amincewar jama’a ga ayyukan tsaro na gwamnati da kuma bata sunan Nijeriya a idon duniya.

DSS ta ce: “Bayanan sirrin da hukumar ta samu sun nuna cewa masu aikata laifuka sun sauya dabarunsu wajen zabar wuraren da za su kai hari.”

Hukumar ta kara gargadin cewa jihar ba za ta iya yin watsi da illolin tsaro da wannan sabon yanayi zai iya haifarwa ba, inda ta bukaci gwamnatin jihar ta gaggauta kara tsaurara matakan tsaro a kusa da manyan makarantu.

Haka kuma, DSS ta bukaci gwamnatin jihar Sokoto da ta dauki matakan da suka dace domin dakile shirin hare-haren da aka gano.

Wannan gargadi ya zo ne a daidai lokacin da rashin tsaro ke ci gaba da addabar wasu sassan Arewa maso Yamma, inda hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane ke ci gaba da barazana ga al’ummomin karkara da cibiyoyin ilimi.

Sabon gargadin ya kara jawo hankalin jama’a kan tsaron dalibai da ma’aikata a jami’o’i, kwalejojin fasaha, kwalejojin ilimi da sauran manyan makarantu da ke fadin jihar Sokoto.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata