Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta ce har yanzu ba ta samu cikakken kwafin hukuncin kotun tarayya da ke Lokoja ba, wanda ya soke wani tsohon hukunci da ya umarci ta yi wa jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) rajista.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, mai bai wa shugaban INEC shawara kan yaɗa labarai, Adedayo Oketola, ya ce hukumar ta san da rahotannin da ke yawo a kafafen yaɗa labarai kan hukuncin da kotun ta yanke a ranar 26 ga Yuni, 2026, amma ba za ta iya yin tsokaci kai tsaye ba sai bayan ta samu kwafi na hukuncin.
INEC ta bayyana cewa sashen shari’arta ne zai nazarci hukuncin bayan samun cikakken kwafinsa kafin ta ɗauki matakin da ya dace bisa umarnin kotu.
Kotun tarayya da ke Lokoja ƙarƙashin Mai Shari’a Isah Dashen ce ta soke hukuncin da aka yanke a watan Disamban 2025 wanda ya umarci INEC ta yi wa NDC rajista, bayan ƙungiyar Peace Movement Party ta ce tambarinta ne aka yi amfani da shi wajen samun hukuncin farko ba tare da an saka ta cikin ƙarar ba.
Sai dai jam’iyyar NDC ta yi watsi da hukuncin tare da bayyana shirin ɗaukaka ƙara zuwa kotun daukaka ƙara, inda shugaban jam’iyyar Sanata Moses Cleopas ya ce kotun ba ta da hurumin sake duba hukuncin da ta riga ta yanke kan batun.
