Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin cewa sojojin ƙasarsa sun taimaka wajen kawo ƙarshen kashe-kashen Kiristoci a Nijeriya sakamakon matakan tsaro da suka ɗauka kan masu tayar da ƙayar baya.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, Trump ya faɗi haka ne a wani taro da aka gudanar a birnin Washington ranar Juma’a, inda ya yi magana kan ayyukan tsaro da gwamnatin Amurka ke yi domin yaƙi da ta’addanci a sassa daban-daban na duniya.
Shugaban na Amurka ya ce hare-haren da suka kai sun raunana shugabannin waɗanda yake zargi da kai hare-hare kan fararen hula musamman Kiristoci a wasu yankunan Nijeriya da ke fama da matsalar rashin tsaro.
A cewarsa, dubban mutane da suka haɗa da mata da yara da tsofaffi ne suka rasa rayukansu kafin matakan da Amurka ta ɗauka, yana mai cewa sojojin Amurka sun kashe wasu manyan shugabannin ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
