Kasar Isra’ila ta sanar da cewa tana ci gaba da fadada hadin gwiwarta da Nijeriya a bangarorin noma, lafiya, ilimi da kirkire-kirkire, tare da ba da gudummawar motocin daukar marasa lafiya guda uku domin tallafa wa harkokin kiwon lafiya a kasar.
Jaridar Punch ta rawaito Jakadan Isra’ila a Nijeriya, Michael Freeman ne ya bayyana hakan a Abuja yayin bikin cika shekaru 78 da samun ‘yancin kai na kasar Isra’ila.
Freeman ya ce kamfanonin Isra’ila na aiki a Nijeriya a yanzu, inda manoma ke amfani da iri da fasahohin noma na Isra’ila wajen samar da amfanin gona a cikin kasar.
Ya bayyana cewa kayan lambun da aka nuna a wajen bikin an noma su ne daga irin da Isra’ila ta samar tare da amfani da fasahohinta, amma a gonakin Nijeriya kuma ta hannun manoman Nijeriya.
Jakadan ya ce wannan hadin gwiwar na iya taimakawa wajen kara yawan amfanin gona, bunkasa tattalin arzikin karkara da kuma inganta samar da abinci ga miliyoyin mutane a Nijeriya.
Har ila yau, ya sanar da cewa Isra’ila za ta kaddamar da zagaye na biyar na shirinta na bunkasa ‘yan kasuwa a shekarar 2027, domin kara bai wa matasa damar koyon dabarun kasuwanci da kirkire-kirkire.
Freeman ya kuma bayyana cewa motocin daukar marasa lafiya guda uku da Isra’ila ta bayar sun riga sun kama hanya zuwa Nijeriya, inda za su taimaka wajen ceton rayuka musamman a lokutan bukatar gaggawa.
A cewarsa, dangantakar Isra’ila da Nijeriya ba ta tsaya kan taimako kadai ba, illa tana da nufin samar da makoma mai kyau ga kasashen biyu ta hanyar hadin gwiwa a fannoni daban-daban.
Da take jawabi a wajen taron, Ministar fasaha, al’adu da yawon bude ido ta Nijeriya, Hannatu Musawa, ta taya gwamnatin da al’ummar Isra’ila murnar cika shekaru 78 da samun ‘yancin kai, tare da jaddada kudirin Nijeriya na kara karfafa dangantaka da kasar.
Ta ce kasashen biyu na da kyakkyawar alaka mai tushe a kan hadin gwiwa, bunkasa tattalin arziki da mutunta juna, tana mai bayyana cewa al’adu da yawon bude ido na daga cikin hanyoyin da za su kara kusantar da al’ummomin kasashen biyu.
