Kwamitin zartarwa na kasa na jam’iyyar APC ya fara daukar matakan dakile cece-kuce da korafe-korafen da suka biyo bayan zabukan fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar a wasu jihohin Nijeriya.
Rahotanni sun nuna cewa kwamitin na shirin mika sunayen ‘yan takarar da suka samu nasara a zabukan fidda gwani ga hukumar zabe ta kasa INEC, yayin da take kokarin sasanta bangarorin da ke rikici domin kauce wa rabuwar kai a cikin jam’iyyar.
Wannan mataki na zuwa ne bayan da wasu ‘yan takara da magoya bayansu suka nuna rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da zabukan fidda gwani, lamarin da ya haifar da korafe-korafe da zarge-zarge a wasu jihohi.
Majiyoyi daga jam’iyyar sun bayyana cewa shugabannin APC na kasa na son a kawo karshen takaddamar cikin gaggawa domin jam’iyyar ta mayar da hankali kan shirye-shiryen zabukan 2027.
Haka kuma, ana sa ran shugabannin jam’iyyar za su ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa rikice-rikicen da suka taso ba su yi tasiri ga hadin kan jam’iyyar ba.
