Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a a Nijeriya JAMB, ta sanar da dakatar da dukkan shirye-shiryen digiri da ake gudanarwa a kwalejojin ilimi masu alaƙa da jami’o’i, inda ta ce daga zangon karatu na 2026/2027, NCE ce kadai za ta zama hanyar shiga kwalejojin.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin sabbin ka’idojin rajista na NCE/ND Agric da ofishin Rajistar hukumar ya fitar a watan Yunin 2026, inda ta ce babu sauran yin digiri a kowace kwalejin ilimi mai alaƙa da jami’a.
JAMB ta kuma jaddada cewa daga wannan lokaci, ba za a ƙara karɓar ɗalibai kai tsaye zuwa matakin aji daya ko biyu a kwalejojin ilimi ba, sai dai ta hanyar shirin NCE kawai.
Hukumar ta ce wannan sabon tsarin zai kawo ƙarshen dogon lokaci da kwalejojin ilimi ke amfani da alaƙa da jami’o’i wajen ba da digiri ga ɗalibai.
Ta bayyana cewa matakin zai shafi dubban ɗalibai da suka riga suka zaɓi kwalejojin ilimi domin karatun digiri a tsarin shigar 2026.
Domin rage tasirin sauyin, JAMB ta ce ɗaliban da abin ya shafa za su iya sauya cibiyar karatu ba tare da biyan kuɗi ba, ko kuma a tura su jami’ar da ke da alaƙa da shirin digirin da suka zaɓa.
Hukumar ta kuma ba da damar ɗalibai su mai da zaɓinsu na biyu ya zama na farko ko kuma su koma shirin NCE idan sun so.
Ta ce waɗanda suka zaɓi NCE za su biya kuɗin rajista na ₦700 tare da samun lambar tantance O’Level daga hukumar da ta dace.
Hukumar ta bukaci dukkan cibiyoyi, da na jarabawar kwamfuta CBT da jami’anta a fadin ƙasar su bi sabbin ƙa’idojin sosai domin tabbatar da cikakken aiki da doka.
Wannan sabon tsari na nufin kawo sauyi mai girma a tsarin koyar da malamai a Nijeriya, inda NCE zai zama hanya tilas kafin shiga aikin koyarwa ko ci gaba zuwa matakin ilimi mafi girma.
