Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta ce ta ƙwato dabbobi 117 bayan jami’an tsaro sun daƙile wani yunƙurin satar shanu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a Ƙaramar Hukumar Charanchi.
Kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq-Aliyu, ya ce lamarin ya faru ne bayan samun sahihan bayanan sirri cewa ’yan bindiga sun kai hari kauyukan Saburu da Billiri tare da kwashe dabbobi.
Ya ce DPOn Charanchi ya jagoranci jami’an ’yan sanda tare da sojoji da jami’an Katsina State Community Watch Corps domin bin sawun maharan.
A cewarsa, jami’an tsaron sun tare hanyoyin tserewar ’yan bindigar, lamarin da ya kai ga musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu.
Ya ce ƙarfin wutar da jami’an tsaro suka nuna ya tilasta wa ’yan bindigar barin dabbobin da suka sace tare da tserewa cikin daji.
Rundunar ta ce an ƙwato shanu 43 da tumaki 74, wanda ya kawo jimillar dabbobin da aka ceto zuwa 117.
Ta ƙara da cewa ana ci gaba da farautar ’yan bindigar da suka tsere domin cafke su.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, Aliyu Umar-Fage, ya yaba wa jami’an tsaron bisa haɗin gwiwar da suka nuna wajen gudanar da aikin.
Ya kuma buƙaci al’ummar jihar su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin ƙarfafa yaƙi da masu aikata laifuka.
Rundunar ta jaddada aniyarta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Katsina.
