DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijeriya ta yanke wa mutane 1,721 da ake zargi da manyan...

Gwamnatin Nijeriya ta yanke wa mutane 1,721 da ake zargi da manyan laifuka hukunci – Nuhu Ribadu

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta samu hukuncin daurin masu laifukan ta’addanci 1,721 tun bayan fara shirin shari’o’in ta’addanci a watan Oktoban 2017.

Daraktan Harkokin Shari’a na Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA), Zakari Mijinyawa, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai na hukumomin tsaro a Abuja.

Ya ce an kammala matakai 10 na shari’o’in, inda aka kuma sallami ko wanke waɗanda ba a samu isassun hujjojin da za su tabbatar da laifinsu ba.

A cewarsa, matakai na tara da na goma da aka gudanar a shekarar 2026 sun samar da hukunci 865, wanda ya zarce jimillar hukunci 856 da aka samu a matakai tara na baya.

Hedikwatar Tsaro kuwa ta ce sojoji sun hallaka mayaƙa da ’yan bindiga 1,597, sannan sun ceto mutane 1,516 da aka yi garkuwa da su tsakanin Janairu da Yuni na bana.

Ta ce an gudanar da ayyukan tsaro 14,221 a sassa daban-daban na ƙasar, inda aka ƙwato bindigogi 451, harsasai 16,726 da bama-bamai.

Haka kuma, sojoji sun ce mayaƙan Boko Haram da ISWAP 132 sun miƙa wuya sakamakon matsin lambar da ake ci gaba da yi musu.

A nata ɓangaren, Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta ce ta kama mutane da dama da ake zargi da ta’addanci, garkuwa da mutane da fashi da makami.

’Yan sandan sun kuma ce sun tarwatsa wasu ƙungiyoyin masu aikata laifuka, tare da ƙwato makamai da kayan gwamnati da aka sace.

Hukumomin tsaron sun buƙaci ’yan Nijeriya su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da sauran laifuka a faɗin ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata