Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Sanata Adolphus Wabara ya nada wani kwamitin gudanarwa na wucin gadi mai mutum 13 domin tafiyar da harkokin jam’iyyar.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa an ɗauki wannan mataki ne domin cike giɓin shugabanci da ya biyo bayan hukuncin Kotun koli.
Wabara ya bayyana cewa hukuncin Kotun koli da ya soke babban taron zaɓen shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan ne ya haifar da gibin shugabanci, wanda ya tilasta ɗaukar wannan matakin gaggawa.
Sabon kwamitin na wucin gadi wanda ya ƙunshi mutum 13, tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Tanimu Turaki, ne zai jagoranta domin tafiyar da harkokin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a warware matsalolin cikin gida.
An yanke wannan shawara ne a wani taron Kwamitin zartarwar jam’iyyar na kasa NEC.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da rikice-rikicen cikin gida ke ƙara kamari a jam’iyyar, musamman tsakanin ɓangarori daban-daban da ke ikirarin shugabancinta.
Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa wannan sabon kwamitin na iya zama wani yunƙuri na dawo da zaman lafiya da daidaito a jam’iyyar, ko kuma yana ƙara tsananta rikicin idan ba a samu haɗin kai ba.
