Ministan Kuɗi kuma Ministan da ke Kula da Tattalin Arziƙin Nijeriya, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa rangwamen farashin man fetur da Kamfanin NNPC ya fara bayarwa ba wai dawo da tallafin man fetur ba ne, yana mai cewa ba a yi amfani da kuɗin gwamnati wajen gudanar da shirin.
Oyedele ya ce rangwamen, wanda aka fara aiwatarwa a ranar 1 ga Oktoba, 2026, yana fitowa ne daga ribar da kamfanin ke samu wajen sayar da fetur, ba daga kasafin kuɗin gwamnatin tarayya ko asusun haɗin gwiwar tarayya ba.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta fitar ranar Juma’a, ministan ya bayyana cewa tsarin na bai wa kamfanin damar rage ribar da yake ƙarawa kan farashin fetur, sannan ya miƙa wannan rangwame ga masu sayen mai.
Ya ce wannan tsari ya bambanta da tallafin man fetur, inda gwamnati ke biyan wani kaso na kuɗin man domin rage farashin da masu saye za su biya a gidajen mai.
A cewarsa, gwamnatin yanzu ta kawo ƙarshen tsarin tallafin man fetur a shekarar 2023, yana mai jaddada cewa rangwamen da ake bayarwa a yanzu ba a amfani da kuɗaɗen jama’a waɗanda za a iya amfani da su wajen biyan albashi, gina makarantu, samar da asibitoci da sauran ababen more rayuwa.
Oyedele ya bayyana cewa NNPC na sayen fetur daga matatar mai ta Dangote da sauran masu samar da man a farashin kasuwa, kafin ta ƙara ribarta domin tantance farashin da za ta sayar da shi a gidajen mai.
Ya ce matakin rage wannan riba dabarar kasuwanci ce da aka ɗauka domin rage wa masu ababen hawa nauyin kuɗin fetur tare da ƙarfafa harkokin kasuwancin kamfanin.
Ministan ya ƙara da cewa rangwamen na iya ƙara ribar NNPC da kuma kuɗaɗen rarar ribar da take turawa ga Gwamnatin Tarayya, sakamakon karuwar yawan man da mutane za su saya da kuma samun amincin kwastomomi.
Ya kuma yi watsi da damuwar cewa rangwamen zai iya ƙarfafa safarar fetur ba bisa ƙa’ida ba zuwa ƙasashen waje ko kuma ya kawo cikas ga kasuwar man fetur, yana mai cewa ribar dillalan fetur ba ta kai kashi biyar cikin ɗari na farashin man da ake sayarwa ba.
A cewarsa, farashin fetur a ƙasashen da ke makwabtaka da Nijeriya ya riga ya fi na Najeriya da kashi 20 zuwa 40 cikin ɗari, don haka rangwamen ba zai haifar da babban gibi tsakanin farashin man a Nijeriya da na waɗannan ƙasashe ba.
Oyedele ya ce gwamnati na ɗaukar wasu matakai domin rage wa gidaje da ‘yan kasuwa nauyin tsadar man fetur, ciki har da faɗaɗa zirga-zirgar ababen hawa masu amfani da iskar gas ta CNG, cire wasu haraji da kuɗaɗen fito kan fetur, da kuma kawar da haramtattun kuɗaɗen da ake karɓa waɗanda ke ƙara tsadar sufuri.
