Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya soki ’yan siyasar adawa da ke neman kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, yana mai tambayar yadda za su iya jagorantar ƙasa idan sun gaza tabbatar da haɗin kai a cikin jam’iyyunsu.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin bikin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban kasa na jam’iyyar APC a zauren Banquet Hall da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce masu iƙirarin ceto Nijeriya ya kamata su fara nuna cewa za su iya shawo kan saɓanin ra’ayi da kuma sasanta rikice-rikicen da ke tsakanin shugabannin jam’iyyunsu.
Shettima ya tambayi yadda ’yan siyasar da ke fuskantar matsalar sasanta ’yan jam’iyyarsu kaɗan za su iya daidaita muradun al’ummar ƙasa mai mutane sama da miliyan 200.
Ya bayyana zaɓen 2027 a matsayin wata dama da ’yan Nijeriya za su tantance ƙwarewa, ɗabi’a da kuma manufofin mutanen da ke neman shugabancin ƙasar.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma buƙaci mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC da su mayar da hankali kan tsara ayyukansu, gamsar da masu zaɓe da kuma samar da sakamakon da za a iya aunawa, maimakon musayar kalamai da abokan hamayya.
Ya ce ya kamata kowace ƙaramar hukuma da al’umma su fahimci manufofin APC, tare da sauraron koke-koken jama’a cikin haƙuri da kuma ɗaukar matakan da suka dace.
Shettima ya kare manufofin tattalin arzikin Tinubu
mataimakin shugaban ƙasar ya kuma kare matakan tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, musamman cire tallafin man fetur da sauye-sauyen da aka yi a tsarin canjin kuɗin waje.
Shettima ya ce Tinubu ya karɓi ragamar mulki ne a lokacin da tattalin arzikin ƙasar ke fuskantar matsaloli masu tsanani, yana mai cewa gyare-gyaren sun buƙaci ɗaukar matakai masu wahala da gwamnatocin baya suka kauce wa ɗauka.
A cewarsa, cire tallafin man fetur da sauya tsarin canjin kuɗi na daga cikin matakan da gwamnatin ta ɗauka domin rage matsalolin tattalin arziki da kuma samar da ginshiƙin ci gaba a nan gaba.
Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta fifita abin da take ganin zai amfani tattalin arzikin ƙasar a dogon lokaci, maimakon mayar da hankali kan samun karɓuwa a wajen jama’a cikin gaggawa.
