Jürgen Klopp ya dawo aikin horas da ƙwallon ƙafa bayan an nada shi sabon babban kocin tawagar ƙasar Jamus.
Rahotannin da jaridar Punch ta ambato sun ce Klopp ya amince da yarjejeniya ta dogon lokaci da za ta sa ya jagoranci tawagar Jamus har zuwa watan Yulin 2030. Wannan na nufin komawarsa kan aikin horas da ƙungiya bayan ya yi fice a matsayin mai horaswa a matakin kulob.
A wani saƙo da aka wallafa a shafin X na Fabrizio Romano a ranar Juma’a, an tabbatar da cewa Klopp ya amince ya zama sabon kocin Jamus, tare da yarjejeniyar da za ta ci gaba har zuwa 2030.
Klopp, wanda ya taba jagorantar Borussia Dortmund da Liverpool, na daga cikin fitattun masu horaswa a zamaninsa. Ya kuma shahara da salon wasan ƙwallon ƙafa da ƙwarewar jagoranci da kuma iya haɓaka ƙwararrun ‘yan wasa.
A lokacin da yake jagorantar Liverpool, Klopp ya lashe manyan kofuna da dama, ciki har da gasar zakarun Turai ta UEFA Champions League, Premier League, FIFA Club World Cup, UEFA Super Cup, FA Cup da League Cup.
A Borussia Dortmund kuma, ya lashe Bundesliga sau biyu a jere, tare da gina ƙungiyar da ta zama ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Turai.
Nadin Klopp a matsayin kocin tawagar Jamus shi ne babban aikinsa na farko a matakin horar da tawagar ƙasa. Yanzu ana sa ran zai jagoranci Jamus wajen gina sabuwar tawaga mai ƙarfi da kuma ƙoƙarin dawo da ƙasar cikin sahun manyan ƙasashen ƙwallon ƙafa na duniya.
