DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, April 21, 2026
HomeSiyasaKa ci gaba da zama a ADC, ka yaƙe su, ka tarwatsa...

Ka ci gaba da zama a ADC, ka yaƙe su, ka tarwatsa mana su — Gbajabiamila ga Abejide

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Nijeriya, Femi Gbajabiamila, ya buƙaci ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, da ya ci gaba da zama a jam’iyyar adawa ta ADC tare da ƙarfafa gwagwarmayarsa a cikinta.

Gbajabiamila ya bayyana hakan ne yayin da yake yaba wa irin rawar da Abejide ke takawa a siyasar majalisa, yana mai cewa abin da yake yi yana da tasiri.

Ya ce ya kamata Abejide ya tsaya tsayin daka, ya ci gaba da fafutuka tare da ƙarfafa matsayinsa a cikin jam’iyyar.

A cewarsa, irin wannan jajircewa na taimakawa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya da samar da sahihin wakilci a majalisa.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sauya sheƙa tsakanin ‘yan majalisa gabanin zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata