Sanata Ali Ndume ya nemi Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya kasafin kuɗin rundunar sojin Nijeriya cikin First-Line Charge, domin kauce wa jinkirin sakin kuɗaɗen ayyukan soji.
Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce tsarin kasafin kuɗin da ake amfani da shi a yanzu na haifar da tsaiko tsakanin ma’aikatar tsaro da ma’aikatar kuɗi, lamarin da ke kawo cikas ga ayyukan sojojin da ke yaƙi da ta’addanci da ’yan bindiga.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sanata Ali Ndume, tsohon shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojoji, ya fitar a ranar Laraba, inda ya kuma yabawa Shugaba Tinubu kan amincewa da ƙarin albashi ga wasu rukunin jami’an tsaro.
Ƙarin albashin, wanda zai kasance tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin 100, zai shafi kusan jami’an soji 250,000 daga watan gobe. Ndume ya ce matakin zai ƙara wa jami’an soji ƙwarin gwiwa, musamman bayan ƙara yawan rundunonin soji daga takwas zuwa 12.
Sai dai Sanata Ndume ya ce ƙarin albashi kaɗai bai isa ba, yana mai buƙatar gwamnati ta tabbatar da samar da makamai, alburusai da sauran kayan aikin da sojoji ke buƙata a kan lokaci, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce: “Duk waɗannan za a iya cimma su cikin sauƙi idan aka sanya kasafin kuɗinsu na shekara cikin First-Line Charge. Wannan tsarin kasafin kuɗi na yanzu, yana cikin tsari mai cike da tsaiko tsakanin ma’aikatar tsaro da ma’aikatar kuɗi.”
Ndume ya kuma buƙaci Shugaba Tinubu ya samar da tsarin da zai ba sojoji damar samun kuɗaɗen aikinsu kai tsaye daga Asusun Tarayya, kamar yadda ake yi wa wasu hukumomin gwamnati.
A cewarsa, irin wannan tsari zai taimaka wajen tabbatar da cewa sojoji sun samu kuɗaɗen da suke buƙata cikin lokaci, tare da ƙarfafa ikonsu na tunkarar barazanar tsaro a sassa daban-daban na Nijeriya.
