DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeKetareAmurka ta kori baƙi sama da miliyan uku cikin watanni 15

Amurka ta kori baƙi sama da miliyan uku cikin watanni 15

Gwamnatin Amurka ta ce ta kori sama da baƙi miliyan uku daga ƙasar cikin watanni 15 tun bayan komawar Shugaban Amurka, Donald Trump, kan mulki.

Wannan na ƙunshe cikin wani bayani da Fadar White House ta wallafa a ranar Laraba, inda gwamnatin ta bayyana matakan da ta ce ta ɗauka domin gyara tsarin shige da fice na ƙasar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnatin Trump ta ce cikin watanni 15 a jere ba ta sake sakin wani baƙon da ya shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba cikin Amurka ba, yayin da ta kori sama da mutum miliyan uku, ciki har da dubban waɗanda aka samu da manyan laifuka.

“Gwamnatin Trump ta kori sama da baƙi miliyan uku da ke Amurka ba bisa ƙa’ida ba, ciki har da dubban waɗanda aka samu da laifukan da suka shafi tashin hankali,” in ji Fadar White House.

Gwamnatin ta kuma ce ta fara wani shiri na kwace ƙasar Amurka daga mutanen da ta ce sun samu takardar zama ɗan ƙasa ta hanyar yaudara, inda aka shigar da ƙara kan mutum 88 da ake zargin ba su cancanci samun wannan matsayin ba.

Ta ce ta kuma dakatar da tallafin gwamnati da ake bai wa sama da baƙi miliyan 1.4 da ba su da takardun zama, tare da hana su shiga wasu shirye-shiryen kiwon lafiya da ake amfani kuɗin masu biyan haraji a ƙasar.

A bangaren biza kuwa, gwamnatin ta ce ta ƙarfafa binciken masu neman bizar Amurka tare da dakatar da samar da bizar ga ƙasashe 75 da ta ayyana a matsayin masu haɗarin tsaro.

Fadar White House ta ce ta kuma ɗauki matakan cire dubban baƙin da ba su da takardun zama daga jerin masu kaɗa kuri’a a wasu jihohin Amurka, tana mai cewa kaɗa kuri’a haƙƙi ne da aka tanadar wa ‘yan ƙasar.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata