Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya yi kira ga ‘yan siyasa a cikin tafiyar jam’iyyar APC da su guji rikici da tada zaune tsaye yayin da harkokin siyasa ke kara zafi a kasar.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, Shettima ya bukaci a nuna da’a da kame kai a dukkan matakai, yana mai cewa tuntuba ta fara, ‘yan takara na neman goyon baya, dattawa na karbar baki, magoya baya na kokarin jawo hankalin wakilai, wanda ke nuna cewa fafatawar siyasa ta sake dawowa.
Ya bayyana wannan lokaci a matsayin hujjar cewa dimokuradiyya na nan daram, inda iko ke ci gaba da kasancewa abin da ake nema ta hanyar tattaunawa, fafatawa, lallashi da kuma cancanta.
Ya ce duk da bambancin buri, magoya baya, yankunan tasiri da ra’ayoyi, hakan abu ne na dabi’a a tsarin dimokuradiyya, domin ba a kirkiro dimokuradiyya don kawar da buri ba, sai dai don koyar da yadda za a fafata ba tare da lalata juna ba, a yi sabani ba tare da tsangwama ba, kuma a amince da rashin nasara ba tare da kona dandalin da ya ba kowa damar bayyana kansa ba.
Don haka ya yi kira ga ‘yan siyasa da su guji fadawa tarkon rudin kafofin yada labarai, masu haddasa rikici, masu son anfani na kansu, ko kuma wadanda ke amfana da rarrabuwar kai.
