DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeKetareDan majalisar Amurka ya soki gwamnatin Tinubu kan tallafin tsaro

Dan majalisar Amurka ya soki gwamnatin Tinubu kan tallafin tsaro

Dan majalisar wakilai na Amurka Riley Moore ya soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Nijeriya bisa zargin gaza cika sharuddan da aka daura kan tallafin tsaro da Amurka ke bai wa Nijeriya.

Moore, wanda ke wakiltar yankin West Virginia na 2, ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a manhajar X a ranar Laraba, inda ya bukaci Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da ya yi la’akari da wannan batu yayin rarraba kasafin kudin shekaru masu zuwa.

Ya ce a ra’ayinsa gwamnatin Tinubu ba ta kai matsayin cika sharuddan da kwamitin kasafi ya gindaya kan tallafin tsaro ba, yana mai kira ga a duba hakan wajen rabon kudaden FY26 da FY27.

Wannan yana nufin shekarun kasafin kudin Amurka da ke farawa daga 1 ga Oktoba zuwa 30 ga Satumba, inda majalisar dokokin kasar ke yanke shawarar yadda za a raba tallafi ga kasashen waje.

Tallafin da ake magana a kai ya hada da horas da sojoji, samar da kayan aiki, hadin gwiwar bayanan sirri da kuma taimako wajen yaki da ta’addanci domin magance matsalolin tsaro kamar tada kayar baya, fashi da makami da kuma aikata manyan laifuka.

Irin wannan tallafi na bukatar amincewar Majalisar Dokokin Amurka, kuma yawanci ana daura masa sharudda kamar bin ka’idojin kare hakkin dan’Adam, gaskiya wajen amfani da kudade, da kuma nuna ci gaba a magance matsalolin tsaro.

Wannan sabuwar suka daga Moore ta biyo bayan wasu kalamai da ya taba yi a baya, inda ya soki gwamnatin Nijeriya kan matsalar tsaro, musamman hare-haren da ke shafar al’ummomin Kirista.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata