Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar da ke neman hana tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 zuwa ranar 11 ga watan Mayun 2026.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Mai shari’a Peter Lifu ne ya ɗage shari’ar bayan lauyan mai ƙara, Ndubuisi Ukpai, ya bayyana wa kotu cewa kwanan nan aka ba su takardar ƙin amincewa da ƙarar daga ɓangaren masu kare Jonathan, kuma suna buƙatar lokaci domin mayar da martani.
Ƙarar na neman kotu ta bayyana ko tsohon shugaban ƙasar na da damar sake tsayawa takara ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999.
A yayin zaman kotun, lauyan Jonathan, Chris Uche SAN, ya ce shi ma ya samu labarin shari’ar ne ta kafafen yaɗa labarai, kuma yana aiki domin tabbatar da cewa an shigar da duk takardun da suka dace a madadin tsohon shugaban ƙasar.
Uche ya kuma tunatar da kotu cewa irin wannan batu an taɓa yanke hukunci a kai a Babbar Kotun Tarayya da Kotun Ɗaukaka Ƙara, yana mai tambayar dalilin sake taso da batun cancantar Jonathan.
Sai dai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC da Babban Lauyan Tarayya, waɗanda ke cikin waɗanda ake ƙara, ba su samu wakilci a kotun ba.
Mai ƙarar, lauya Johnmary Jideobi, na neman kotu ta hana Jonathan sake neman takarar shugaban ƙasa, yana mai hujjar cewa ya riga ya kammala wa’adin da kundin tsarin mulki ya tanada bayan ya karɓi mulki daga marigayi Umaru Musa Yar’Adua a 2010 sannan ya sake cin zaɓen 2011.
Ya ce idan aka bar Jonathan ya sake tsayawa takara kuma ya yi nasara, hakan zai sa ya sake rantsuwa a matsayin shugaban ƙasa karo na uku, abin da ya ce kundin tsarin mulki bai yarda da shi ba.
