DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabaraiKotu ta hana NBC hukunta gidajen rediyo da talabijin kan ra’ayoyi

Kotu ta hana NBC hukunta gidajen rediyo da talabijin kan ra’ayoyi

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta hana Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC) amfani da sabon umarninta wajen hukunta kafafen yaɗa labarai ko masu gabatar da shirye-shirye saboda bayyana ra’ayoyi.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, Mai shari’a Daniel Osiagor ne ya bayar da umarnin wucin gadi ranar Litinin bayan sauraron ƙarar da ƙungiyar SERAP da Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) suka shigar.

Daily Trust ta ruwaito cewa ƙungiyoyin biyu sun kalubalanci wasu sassan dokar NBC da suka ce na bai wa hukumar damar hukunta gidajen rediyo da talabijin saboda bayyana ra’ayi, rashin tsaka-tsaki ko kuma tsawatar wa baki.

Kotun ta umarci NBC da jami’anta da kada su sanya tara ko wani hukunci ga kafafen yaɗa labarai bisa wasu sassan dokar Nigeria Broadcasting Code har sai an kammala sauraron shari’ar.

SERAP da NGE sun bayyana hukuncin a matsayin babbar nasara ga ‘yancin faɗar albarkacin baki da ‘yancin aikin jarida a Nijeriya.

Ƙungiyoyin sun ce aikin jarida ba zai yiwu ba tare da sharhi, nazari da bayyana ra’ayi ba, suna masu cewa dokokin NBC na iya zama wata hanya ta takura wa kafafen yaɗa labarai.

Sun kuma yi gargadin cewa idan ba a dakatar da matakan NBC ba, hakan na iya shafar yadda kafafen yaɗa labarai za su gudanar da aikinsu gabanin zaɓen 2027.

An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 1 ga Yunin 2026.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata