DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiKotu ta samu tsohon Ministan Lantarki da laifin almundahanar kuɗaɗen Mambilla da...

Kotu ta samu tsohon Ministan Lantarki da laifin almundahanar kuɗaɗen Mambilla da Zungeru

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta samu tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, da laifin almundahana da wanke kuɗaɗe a shari’ar da Hukumar EFCC ta shigar a kansa.

Mai shari’a James Omotosho ya bayyana cewa EFCC ta gabatar da hujjoji masu ƙarfi da suka tabbatar da laifin tsohon ministan ba tare da wata shakka ba.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa kotun ta ce Saleh Mamman, wanda ya yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai kusan naira biliyan 33.8.

Kotun ta same shi da laifin biyan dala 655,700 domin sayen wani gida a Abuja ba tare da amfani da banki ba.

Haka kuma an same shi da laifin wawure kuɗaɗen ayyukan lantarki na Mambilla da Zungeru da gwamnatin tarayya ta fitar.

Mai shari’a Omotosho ya ce mafi yawan kuɗaɗen an karkatar da su ne ta hannun masu canjin kuɗi (BDC) waɗanda suka mayar da su dala tare da miƙa wa wanda ake zargi.

Ya ce, “Maimakon ya bar tarihin gyara matsalar wutar lantarki a Nijeriya, wanda ake ƙarar ya kasance yana rayuwa cikin jin daɗi a kan wahalar talakawa.”

Sai dai Saleh Mamman bai halarci zaman kotun lokacin yanke hukuncin ba, lamarin da ya sa kotun ta bayar da umarnin kamo shi bayan amincewa da bukatar EFCC.

Lauyan wanda ake ƙarar ya shaida wa kotu cewa ba a san inda Mamman yake ba tun bayan sanar da ranar hukunci, sai dai mataimakinsa ya ce ba ya da lafiya.

Kotun ta sanya ranar 12 ga Mayun 2026 domin aiwatar masa hukunci.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata