Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke belin da ta bai wa, Omoyele Sowore, tare da bayar da sammacin kama shi bayan ya gaza halartar zaman shari’ar da ake yi masa kan zargin cin zarafin Tinubu a yanar gizo.
Mai shari’a, Mohammed Umar, ya yanke hukuncin ne bayan lauyan masu gabatar da ƙara, Akinlolu Kehinde (SAN), ya buƙaci kotun ta soke belin Sowore saboda rashin bayyana a kotu ba tare da gamsashshiyar hujja ba.
An bayyana wa kotun cewa Sowore da lauyansa ba su halarci zaman ba, sai dai an aike da wasiƙar neman a ɗage shari’ar.
Sa’annan jaridar Premium Times ta ruwaito yadda masu gabatar da ƙara suka yi fatali da buƙatar, suna mai cewa babu wani dalili mai ƙarfi da aka gabatar domin neman ɗage zaman.
Sowore dai na fuskantar shari’a ne bisa zargin wallafa saƙonni a shafukan sada zumunta na X da Facebook inda ake zarginsa da kiran Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da suna mummunan suna.
Bayan sauraron ƙorafin masu gabatar da ƙara, kotun ta amince da buƙatar soke belin tare da bayar da umarnin kama Sowore domin tabbatar da gabatar da shi a gaban kotu domin ci gaba da shari’ar.
