DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeBinciken Gaskiya (Fact Check)Yawan masu amfani da 5G a duniya ya haura biliyan uku -...

Yawan masu amfani da 5G a duniya ya haura biliyan uku – Ericsson

Kamfanin sadarwa na Ericsson ya bayyana cewa yawan masu amfani da fasahar sadarwar zamani ta 5G a duniya ya kai biliyan 3.1 a zangon farko na shekarar 2026.

Hakan na kunshe ne cikin rahoton Mobility Report na watan Yuni 2026, wanda ya nuna cewa an samu karin sabbin masu amfani da 5G miliyan 162 tsakanin watan Janairu da Maris na shekarar nan.

Rahoton ya ce ci gaban ya nuna yadda bukatar intanet mai sauri da ingantacciyar hanyar sadarwa ke ci gaba da karuwa a duniya, yayin da kasashe da kamfanonin sadarwa ke zuba jari wajen fadada ayyukan 5G.

Ericsson ta bayyana cewa fasahar 5G na taimakawa wajen inganta ayyukan sadarwa, bunkasa tattalin arzikin zamani, da samar da sabbin damammaki a fannoni kamar masana’antu, kiwon lafiya, ilimi da sufuri.

Kamfanin ya kuma yi hasashen cewa adadin masu amfani da 5G zai haura biliyan 6.4 nan da shekarar 2031, yayin da fasahar ke ci gaba da yaduwa a kasashe masu tasowa da masu karfin tattalin arziki.

Masana sun ce ci gaba da fadada hanyoyin sadarwa na 5G zai taka muhimmiyar rawa wajen hanzarta sauyin fasaha da bunkasar tattalin arziki a sassa daban-daban na duniya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata