DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeSiyasaKotu ta umurci a tsare malamin jami'a da ake zargi da ɓata...

Kotu ta umurci a tsare malamin jami’a da ake zargi da ɓata sunan Gwamnatin Katsina

Babbar Kotun Majistare da ke Katsina ta ba da umarnin tsare Dr. Bashir Kurfi, malami a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, bayan rundunar ‘yan sandan Jihar ta gurfanar da shi bisa zargin ɓata suna da kuma yaɗa bayanan ƙarya masu tayar da hankali kan gwamnatin jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘Yan sanda sun ce Dr. Kurfi ya yi iƙirarin a wata hira da ya yi a Trust TV cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki nauyin wasu ‘yan bindiga zuwa aikin Hajji, zargin da gwamnati ta musanta.

Bayan ya musanta laifukan da ake tuhumarsa da su, lauyansa ya nemi a ba shi beli, amma kotu ta umarci a ci gaba da tsare shi a hannun ‘yan sanda tare da ci gaba da bincike.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 14 ga Yulin, 2026. A gefe guda kuma, kwanaki bayan wannan zargi ya fito, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa jami’an DSS sun kama wasu da ake zargin shugabannin ‘yan bindiga ne yayin da suke dawowa daga aikin Hajji a Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’Adua a Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata