DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeSiyasaKotun Kolin Nijeriya ta jinkirta yanke hukunci kan rikicin shugabancin ADC

Kotun Kolin Nijeriya ta jinkirta yanke hukunci kan rikicin shugabancin ADC

Kotun Koli ta Nijeriya ta jingine hukunci a karar da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ya shigar kan rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar ADC.

Jaridar Punch ta rawaito cewa kotun kolin mai alkalai biyar karkashin jagorancin Justice Mohammed Garba ta dauki matakin ne bayan bangarorin da ke rikicin sun gabatar da rubutattun hujjojinsu na karshe, inda aka ce za a sanar da ranar yanke hukunci nan gaba.

David Mark, wanda ke jagorantar wani bangare na jam’iyyar, yana kalubalantar hukuncin Kotun ɗaukaka kara na ranar 12 ga Maris, wanda ya umarci kowa ya tsaya a inda yake a rikicin.

Shari’ar ta samo asali ne daga wasu mambobin jam’iyyar da suka nuna rashin gamsuwa, karkashin jagorancin Nafiu Bala Gombe, wadanda ke kalubalantar sahihancin shugabancin bangaren Mark.

Sauran wadanda ke cikin karar sun hada da jam’iyyar ADC kanta, sakatarenta na kasa Rauf Aregbesola, da kuma hukumar zaɓen Nijeriya INEC, da tsohon shugaban jam’iyyar Ralph Nwosu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata