Tsohon Ministan Kudi kuma mai kula da harkokin Tattalin Arziki, Wale Edun, ya bayyana cewa yana alfahari da nasarorin da ya samu yayin da yake kan kujera, bayan sauke shi daga mukaminsa.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ne ya sauke Edun daga mukaminsa a ranar Talata, inda ya daga Taiwo Oyedele zuwa matsayin sabon Ministan Kudi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar bayan ficewarsa, Edun ya gode wa Shugaban bisa damar da aka ba shi tun daga shekarar 2023, inda ya fara aiki a matsayin shugaban kwamitin mika mulki, sannan mai ba da shawara kan harkokin kudade, kafin daga bisani ya zama Minista.
Ya ce a lokacin da ya karbi mulki, tattalin arzikin Nijeriya na cikin mawuyacin hali, amma sauye-sauyen da aka yi sun fara haifar da sakamako mai kyau.
Ya kara da cewa tattalin arziki ya bunkasa daga kusan kashi 2% zuwa sama da 4%, yayin da hauhawar farashi ya ragu daga kusan 35% zuwa 15%.
Ya danganta wannan da kokarin da aka yi wajen daidaita tattalin arziki, inganta tsarin kudade, da kuma karfafawa masu zuba jari.
