Hukumar zaɓen Nijeriya INEC za ta ɗage takunkumin da aka sanya kan fara kamfen ɗin zaɓen Shugaban Kasa da na ‘yan majalisar Kasa na 2027 ranar Laraba, 19 ga Agusta, 2026.
A cewar jaridar Daily Trust, jadawalin INEC ya nuna cewa za a gudanar da zaɓen Shugaban Nijeriya da na Majalisar Kasa ranar 16 ga Janairu, 2027, yayin da kamfen ɗin zaɓen gwamnoni da majalisun dokokin jihohi zai fara ranar 9 ga Satumba, 2026.
Jaridar ta yi kira ga jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu da su gudanar da kamfen bisa doka, tare da mayar da hankali kan manufofi da abubuwan da suka shafi rayuwar al’umma, maimakon kalaman batanci, ƙiyayya ko rarrabuwar kawuna.
Jaridar ta kuma yi kira ga ’yan siyasa da su guji amfani da ’yan daba ko wasu masu aikata laifuka wajen cimma manufofin siyasa, tana mai cewa tashin hankali a lokacin zaɓe na iya yin barazana ga zaman lafiya da dimokuraɗiyya.
An kuma buƙaci jami’an tsaro da su kasance masu ƙwarewa, adalci da rashin nuna bambanci wajen gudanar da ayyukansu, tare da tabbatar da cewa tsaro ba zai zama hanyar tsoratar da masu zaɓe ko hana su amfani da haƙƙinsu ba.
Daily Trust ta jaddada cewa ya kamata sojoji su taka rawar da ta dace wajen tsaron zaɓe, yayin da ’yan sanda za su mayar da hankali kan babban aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin jama’a da tabbatar da doka.
Haka kuma, Daily Trust ta buƙaci gwamnati a matakin tarayya da jihohi da kada fara kamfen ya sa su yi watsi da ayyukan mulki da nauyin da ke kansu na kula da jama’a.
Ta kuma yi kira ga masu zaɓe da kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen haifar da tashin hankali, inda ta ce ya kamata su nemi ’yan takara su bayyana manufofi da shirye-shiryensu na magance matsalolin Nijeriya.
A ƙarshe, jaridar ta ce dukkan masu ruwa da tsaki — INEC, jam’iyyun siyasa, ’yan takara, jami’an tsaro, kafafen yaɗa labarai, ƙungiyoyin farar hula da masu zaɓe — suna da alhakin tabbatar da cewa zaɓen 2027 ya kasance cikin lumana, gaskiya da amana.
