DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiKu yi aiki da sarakunan gargajiya domin magance matsalar tsaro – Sultan

Ku yi aiki da sarakunan gargajiya domin magance matsalar tsaro – Sultan

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya bukaci sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Sokoto, CP Hayatu Hassan Shaffa, da ya yi aiki kafada da kafada da sarakunan gargajiya domin magance matsalolin tsaro da ke addabar jihar da kasa baki daya.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne yayin da sabon kwamishinan ya kai masa ziyarar girmamawa a fadarsa da ke Sokoto domin sanar da shi fara aikinsa a matsayin shugaban rundunar ’yan sandan jihar.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya fitar, CP Shaffa ya nemi ayi musu addu’a da shawarwari daga Sarkin Musulmin tare da tabbatar da kudirinsa na karfafa alaka tsakanin rundunar ’yan sanda da sarakunan gargajiya wajen tattara bayanan sirri da tabbatar da tsaro a matakin al’umma.

Da yake jawabi, Sarkin Musulmin ya ce sarakunan gargajiya suna da kusanci da jama’a kuma sun fi sanin halin da ake ciki a yankunansu, don haka hadin gwiwa da su zai taimaka wajen samun sahihan bayanan sirri da za su taimaka wajen dakile matsalolin tsaro.

A nasa bangaren, CP Hayatu Hassan Shaffa ya tabbatar wa Sarkin Musulmin cewa rundunar ’yan sanda za ta ci gaba da aiki tare da masarautu da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta tsaro da zaman lafiya a fadin jihar Sokoto.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata