Magoya bayan tauraron ɗan ƙwallon ƙafa ɗan asalin ƙasar Argentina, Lionel Messi, hankalinsu ya tashi bayan an cire shi daga wasa saboda rauni da ya samu yayin da yake taka leda a ƙungiyar Inter Miami.
Rahotanni sun bayyana cewa an sauya Messi ne ana tsaka da wasa bayan ya nuna alamun rashin jin daɗi, lamarin da ya sa ake fargabar ko zai samu lafiya kafin fara gasar cin kofin duniya.
Kocin ƙungiyar Inter Miami da kuma jami’an lafiya sun ce za a gudanar da gwaje-gwaje domin tantance girman raunin da kuma lokacin da zai iya ɗauka kafin ya murmure gaba ɗaya.
