Majalisar Dattawa ta yanke shawarar amfani da tsarin kaɗa ƙuri’a ka tsaye wajen kudirin kafa ‘yan sandan jihohi, bayan na’urar zaɓe ta yanar gizo da aka tanada ta samu matsalar aiki.
An ɗauki wannan mataki ne bayan nuna damuwa cewa wasu sanatoci za su iya rasa damar kaɗa ƙuri’arsu idan aka ci gaba da amfani da na’urar da ke fama da matsala.
A karkashin sabon tsarin, kowane sanata zai tashi tsaye, ya bayyana sunansa, sannan ya fito fili ya bayyana matsayinsa kan kudirin kafa ‘yan sandan jihohi.
Jagoran Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ne ya gabatar da ƙudirin amfani da kaɗa ƙuri’ar kai tsaye, yayin da Jagoran marasa rinjaye na majalisar Sanata Abba Moro, ya mara masa baya.
