Dan majalisar dokokin Amurka mai wakiltar mazabar West Virginia ta 2, Riley Moore, ya yaba da matakin Majalisar Dattawan Nijeriya na amincewa da kudirin gyaran kundin tsarin mulki domin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Moore ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce kafa ‘yan sandan jihohi zai bai wa jihohi damar kare al’ummominsu da kansu, musamman Kiristocin da ke fuskantar hare-hare da musgunawa a wasu sassan Nijeriya.
A cewarsa, ya dade yana kira da a samar da tsarin ‘yan sandan jihohi tun bayan da ya fara bincike kan hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Nijeriya.
Ya ce wannan mataki zai rage dogaro da hukumomin tarayya da ke Abuja wajen magance matsalolin tsaro.
Moore ya kuma yaba wa Bola Ahmed Tinubu saboda goyon bayan da ya bayar wajen ciyar da kudirin gaba, yana mai cewa hakan ya nuna an fara daukar matakai masu muhimmanci domin magance matsalolin tsaro a kasar.
Sai dai ya bayyana cewa har yanzu kudirin na bukatar amincewar akalla kashi biyu cikin uku na majalisun dokokin jihohi kafin ya zama doka kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
A ranar Laraba ne Majalisar Dattawa ta amince da kudirin bayan fiye da kashi biyu cikin uku na sanatoci sun kada kuri’ar goyon baya.
Kudirin ya tanadi kafa rundunar ‘yan sandan jihohi da za ta yi aiki tare da rundunar ‘yan sandan tarayya.
Haka kuma, kudirin ya mtanadi kariya daga amfani da rundunar wajen cin zarafin masu suka ga gwamnatocin jihohi, inda ya bayyana cewa ba za a yi amfani da ita wajen takura wa mutane saboda ra’ayoyinsu ba sai bisa tanadin doka.
