DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiMajalisar wakilan Nijeriya ta bai wa Sufeto Janar wa'adin awa 48 ya...

Majalisar wakilan Nijeriya ta bai wa Sufeto Janar wa’adin awa 48 ya gabatar da shugaban hukumar bogi ta PFIPC

Majalisar Wakilan Nijeriya ta umarci Sufeto Janar na ’yan Sanda, Olatunji Disu, da ya gabatar da Adeyemi Adeniyi, wanda ke ikirarin cewa shi ne Darakta Janar na Hukumar Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC), a gaban kwamitanta cikin awa 48.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa kwamitin binciken ayyukan hukumar ya bayar da umarnin ne a ranar Litinin yayin ci gaba da zaman bincike da ake gudanarwa a harabar majalisar da ke Abuja.

Shugaban kwamitin, Hon. Yusuf Gagdi, ya ce wajibi ne Adeyemi ya bayyana a gaban kwamitin domin amsa tambayoyi kan zargin da ake masa na kirkirar wata hukuma ba bisa doka ba tare da amfani da sunan gwamnatin tarayya.

Kwamitin na binciken yadda aka samu ofishin hukumar PFIPC a cikin Sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja, duk da cewa ba a kafa hukumar ta hanyar doka ba, tare da yadda aka ware mata kasafin kuɗi na naira biliyan 1.32 a kasafin kuɗin shekarar 2026.

Wakilin Sufeto Janar na ’yan sanda, mataimakin kwamishinan ’yan sanda Bashir Abdullahi, ya shaida wa kwamitin cewa rundunar ’yan sanda ta riga ta gurfanar da Adeyemi a gaban babbar kotun tarayya kan tuhume-tuhume guda takwas da suka shafi haɗa baki da zamba.

Ya kuma tabbatar da cewa binciken ya samo asali ne daga ƙorafe-ƙorafen da ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya shigar, inda ake zargin Adeyemi da gabatar da kansa a matsayin Darakta Janar na PFIPC.

A cewar rundunar ’yan sanda, ana kuma zargin Adeyemi da amfani da wannan ikirari wajen neman daukar ma’aikata kusan 300, neman kasafin kuɗi na dala biliyan 1.3 a kasafin shekarar 2026, da kuma shirya wani taron zuba jari na duniya a madadin hukumar da babu ita.

Binciken kwamitin ya kuma gano cewa akwai takardu kusan 29 da ake zargin an ƙirƙira, ciki har da wasu da aka danganta da fadar shugaban kasa, ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, ofishin sakataren gwamnatin tarayya da ma’aikatar kuɗi, waɗanda hukumomin da abin ya shafa suka musanta sahihancinsu.

Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi, ya ce an umarci Sufeto Janar da ya tabbatar Adeyemi ya bayyana a gaban kwamitin da ƙarfe 12 na rana ranar Laraba, domin ci gaba da binciken da majalisar ke yi kan lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata