Akalla mutane huɗu ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sanye da kayan sojoji suka kai hari ƙauyen Unguwan Lalle da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 8:00 na daren Lahadi, inda suka shafe kusan sa’o’i shida suna harbe-harbe, kwasar kayayyaki da kuma sace dabbobin al’umma.
Rahotanni sun ce maharan, waɗanda yawansu ya kai kusan mutum 200, sun kutsa cikin ƙauyen ta hanyoyi daban-daban, lamarin da ya sa mazauna yankin suka yi zaton sojoji ne saboda kayan sojojin da suke sanye da su.
Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun yi ta harbin duk wanda ya yi ƙoƙarin tserewa, sannan suka shiga gidaje da shaguna suna wawushe dukiyoyi tare da yin awon gaba da dabbobi.
Waɗanda aka tabbatar sun mutu sun haɗa da Bilyaminu Wakkala da Danbaki Tulunawa, yayin da sauran mutum biyu da suka mutu suka fito ne daga ƙauyen Kongurus da ke maƙwabtaka da yankin.
Wani mazaunin yankin ya ce harin ya faru ne ƙasa da awa guda bayan da dakarun sojoji da suka kai ɗauki sakamakon wani hari da aka kai da rana suka bar ƙauyen.
Sai dai da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da kashe wani manomi a yankin, amma ya ce har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai samu cikakken bayani kan sabon harin da aka kai wa Unguwan Lalle ba.
