Malaman addinin Musulunci a kananan hukumomin Mani da Bindawa da ke jihar Katsina sun bukaci al’umma da kada su zabi Jamila Abdu–Mani, ‘yar takarar jam’iyyar APC a zaben majalisar wakilai na 2027 a yankin.
Jamila Abdu–Mani, wadda ita ce mai ba Gwamna shawara kan ilimin ‘ya’ya mata da ci gaban yara, ta zama ‘yar takarar da aka zaba sakamakon hadin kai (consensus) a mazabar Mani/Bindawa, bayan da dan majalisa mai ci Ahmad Yusuf da sauran masu neman takara suka janye.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa tun da farko Ahmad Saleh ne ya fito a matsayin dan takarar da aka zaba, amma daga bisani aka sake zama domin duba batun bayan wasu ‘yan takara sun nuna rashin amincewa.
Jam’iyyar APC a jihar ta zabi amfani da tsarin hadin kai wajen fitar da ‘yan takara domin zaben 2027, inda ta kafa kwamitin koli karkashin tsohon Gwamna Aminu Masari.
A ranar Juma’ar da ta gabata, wasu malamai biyu sun nuna damuwa kan yadda aka fitar da Abdu–Mani, inda suka bukaci al’umma da kada su zabe ta.
Wani malami a garin Bindawa, Usman Salisu, ya ja hankalin shugaban karamar hukumar da sauran masu ruwa da tsaki kan lamarin, yana mai kira da a yi adawa da zaben nata, tare da cewa hakan ya saba da koyarwar Musulunci.
