Bangaren kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP da ke goyon bayan Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da nadin kwamitin gudanarwa na rikon kwarya mai mambobi 13 karkashin jagorancin Tanimu Turaki (SAN) a matsayin shugaba.
An cimma wannan matsaya ne a taron NEC na 103 da bangaren Makinde ya shirya a Abuja, bayan kudurin da shugaban PDP na Jihar Edo, Tony Aziegbemi ya gabatar, wanda Clement Fagboyede ya mara wa baya.
Makinde, yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron, ya bayyana cewa bangarensa ba zai gaji ba wajen fafutukar da yake yi.
Sai dai Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, da bangaren da ke goyon bayansa a PDP sun yi watsi da taron, suna masu cewa an gudanar da shi ba bisa ka’ida ba.
Sun kuma yi fatali da batun cewa akwai wani kwamitin rikon kwarya na NWC, suna cewa ba shi da tushe a doka, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A ranar 30 ga Afrilu, Kotun Koli ta yanke hukuncin soke taron kasa na PDP da bangaren Makinde ya gudanar a Ibadan a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, wanda ya samar da shugabancin Turaki.
Da yake mayar da martani ga hukuncin, shugaban kwamitin amintattu (BoT) na bangaren Makinde, Adolphus Wabara, ya ce bisa matsayar kotun koli kan dakatar da sakataren PDP na kasa da bangaren Wike ke goyon baya, Samuel Anyanwu da wasu, jam’iyyar a halin yanzu ba ta da sahihin shugabanci.
