DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeKasuwanciMasu ɗaukar man fetur a matatar Dangote sun ragu, rikicin farashi ya...

Masu ɗaukar man fetur a matatar Dangote sun ragu, rikicin farashi ya ƙara kamari

 

‘Yan kasuwar man fetur sun bayyana cewa sun rage sayen fetur daga matatar Dangote saboda rashin tabbas kan sabon tsarin farashin da suka fara amfani da shi, wanda ya haɗa da sayar da fetur a dalar Amurka.

Wannan mataki ya sa wasu gidajen mai suka dakatar da sayayya a matatar, yayin da ake fargabar tashin farashin fetur idan rikicin Gabas ta tsakiya ya ci gaba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wasu ‘yan kasuwar man fetur sun ce suna jiran a fayyace sabon tsarin farashin da kuma farashin man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje kafin su ci gaba da saye da yawa.

Sai dai, jami’in matatar Dangote ya musanta rahotannin cewa an dakatar da lodin fetur, yana mai cewa har yanzu motocin dakon mai a matatar suna cigaba da kwasan kaya.

Rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne daga sabanin ra’ayi tsakanin Gwamnatin Nijeriya da matatar ta Dangote kan batun ba da lasisin shigo da man fetur da kuma yawan ɗanyen man da ake bai wa matatar, musamman wanda ake sayar mata da kuɗin naira.

A nata ɓangaren, Hukumar kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki ta Ƙasa FCCPC ta jaddada cewa naira ne kaɗai halattaccen kuɗin gudanar da cinikayya a Nijeriya.

Hukumar ta kuma bayyana damuwa cewa raguwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya bai sa saukar farashin fetur ga masu amfani da shi ba, saboda haka za ta ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata