DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabaraiMun kwato bindigogi 676 da harsasai sama da 330,000 a Nijeriya –...

Mun kwato bindigogi 676 da harsasai sama da 330,000 a Nijeriya – DSS

DaDaraktan-Janar na hukumar DSS na hukumar tsaro ta DSS a Nijeriya, Oluwatosin Ajayi, ya bayyana cewa hukumar ta kwato bindigogi 676 da kuma harsasai 332,874 nau’o’i daban-daban tun daga ranar 29 ga Mayun 2023 zuwa yanzu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ajayi ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai, yayin da yake cika shekaru biyu a matsayin Daraktan-Janar na DSS, inda ya ce hukumar na ci gaba da ƙara mayar da hankali kan yaki da ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka.

Ya ce baya ga kwato makamai da harsasai, DSS ta kuma samu nasarorin gurfanar da wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka, inda wasu daga cikinsu suka samu hukuncin daurin rai da rai, yayin da wasu kuma aka yanke musu hukuncin kisa.

Ajayi ya ce hukumar ta sauya salon aikinta wajen mayar da hankali kan tabbatar da doka, tattara hujjoji da kuma gurfanar da masu laifi a gaban kotu, maimakon kama mutane kawai ba tare da samun cikakkun hujjoji ba.

Ya bayyana cewa DSS ta kuma karfafa hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro na cikin gida da abokan hulɗarta na ƙasashen waje, ciki har da hukumomin leken asiri na Amurka, Birtaniya, Faransa da wasu ƙasashen Turai.

Game da kare haƙƙin bil’adama, Daraktan-Janar din ya ce ya umurci jami’an DSS da kada su kama mutum a kan batun da yake na farar hula, ne yana mai cewa irin waɗannan al’amura ya kamata a kai su kotu domin samun fassarar doka.

Ya kuma ce hukumar ta fara biyan diyya tare da tallafa wa mutanen da aka cutar da su sakamakon kuskuren jami’an DSS, yana mai cewa hukumar ta biya sama da Naira miliyan 300 a matsayin diyya a wasu daga cikin irin waɗannan lamuran.

Ajayi ya ce daya daga cikin manyan sauye-sauyen da ya aiwatar shi ne inganta dangantakar DSS da kafafen yaɗa labarai, inda ya bayyana ’yan jarida a matsayin abokan aiki wajen samar da bayanan da suka shafi tsaro ga jama’a da gwamnati.

Ya ce idan DSS ta samu matsala da rahoton da wata kafar yaɗa labarai ta wallafa, matakin farko shi ne neman a gyara ko a janye rahoton, maimakon kama ɗan jarida. Ya ƙara da cewa idan ba a samu mafita ba, hukumar za ta iya neman hakkinta ta hanyar kotu.

Dangane da matsalar rashin tsaro kuwa, Ajayi ya amince cewa hare-haren ta’addanci da sauran laifuka har yanzu suna faruwa, amma ya ce leken asiri ba zai iya dakile duk wani laifi dari bisa dari ba. Ya ce akwai matsalolin yanayi, wuri mai wahalar shiga da kuma bukatar matakan dabarun tsaro da suka dace da kowace al’umma.

Ya goyi bayan matakan kafa ’yan sandan jihohi da kuma farfaɗo da rundunar tsaron dazuzzuka, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen samar da sahihin tsaro a yankunan da ke da nisa daga cibiyoyin gwamnati.

Daraktan-Janar din ya kuma yi gargadin cewa bai kamata a danganta laifi da kabila, addini ko wata al’umma ba, yana mai cewa ya kamata a hukunta mai laifi bisa abin da ya aikata ba tare da la’akari da asalinsa ba.

A cewarsa, daya daga cikin matsalolin da ke kara ta’azzara rashin tsaro shi ne raguwar kyawawan dabi’u da kuma rashin isasshen ikon gwamnati a wasu yankunan karkara, lamarin da ke barin wasu wurare a matsayin mafaka ga masu aikata laifuka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata